Ƙasa d kwanaki 30 bayan ƙaddamar da dakarun tsaro a Jihar Katsina, ‘yan bindiga sun afka ƙauyen Rugar Kusa da ke cikin Ƙaramar Hukumar Musawa, inda suka kashe mutum 14 tare da jikkata wasu 17 a wurin taron Maulidi.
Lamarin ya faru a ranar Lahadi da dare, inda maharan suka shafe awa ɗaya a ƙauyen su na ta’addanci.
Waɗanda harin ya ritsa da su sun bayyana cewa an kai samamen wajen ƙarfe 11 na dare.
“Ana kusa da kammala taron Maulidin kawai sai ga ‘yan ta’adda sun kutso ɗauke da bindigogi su na harbi ta ko’ina.”
Haka wani ya bayyana wa wakilin PREMIUM TIMES, amma ya nemi a sakaya sunan sa, a lokacin da suka yi hira ta wayar tarho.
“Mutane da yawa sun tafi gida sun kwanta barci lokacin da abin ya faru, amma rugugin harbin bindigogi ya tashi kowa daga barci.”
Ganau ya shaida wa wakilin mu cewa wasu maharan sun kewaye masu taron Maulidi su na buɗe masu wuta, wasu kuma suka kutsa cikin ƙauyen su na kashe mutane.
Amma ya ce mutane da dama ciki har da masu taron Maulidi sun tsere cikin daji.
“Mun samu gawarwaki 14, amma dai ba mu sani ba ko akwai sauran wasu gawarwakin ko kuma shin an yi garkuwa da wasu mutanen ko ‘a’a. Saboda har yanzu akwai waɗanda ba mu san halin da suke ciki ba.” Inji shi.
PREMIUM TIMES ta ji daga bakin wani ma’aikacin Asibitin Ƙashi na Ahmadi Rimi da ke Katsina cewa an kai mutane da dama masu ɗauke da raunuka sanadiyyar harbin bindigar da aka yi masu.
Sai dai kuma Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Katsina, ya ce mutum 9 kaɗai aka kashe, kuma 16 aka ji wa rauni ba 17 ba.
Discussion about this post