Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya ce gargaɗin da Amurka ta fitar kan Najeriya ya na kawo babban cikas ga tattalin arzikin ƙasar ƙasa.
Mohammed Idris ya bayyana haka a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a ranar Litinin, a Abuja.
A ranar Juma’a ce Ofishin Jakadancin Amurka da ke Abuja ya fitar da sanarwar “wata babbar barazana” ga manyan otal-otal da ke faɗin Najeriya, amma jami’an tsaron Najeriya na aiki tuƙuru domin daƙile barazanar.
Idris ya ce, ” Abu mafi muhimmanci shi kada a yi wa barazana fassarar dukkan game-garin faɗin ƙasar nan, domin yin hakan ba wani alheri ba ne.”
Ya ƙara da cewa gwamnati a kullum ta na ɗaukar tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a da sauran dukkan maziyarta cikin ƙasar nan.
” Mun fahimci damuwar da Amurka ke nunawa ko kuma ta nuna a cikin gargaɗin da ta fitar. Amma kuma mun haƙƙaƙe cewa bai kamata kuma bai dace a nuna wannan barazanar ta shafi dukkan otal-otal ɗin faɗin ƙasar nan ba.
Sai kuma kawo illa ga tattalin arzikin ƙasa da gargaɗin ke yi. Sannan kuma ya kan zama wata hanyar yi wa ƙoƙarin da gwamnati ke yi na samun masu zuba jari a cikin ƙasa zagon-ƙasa.
“A kullum mu na bayar da fifiko wajen kare rayuka da lafiyar duk wasu baƙin da suka kawo ziyara cikin ƙasar nan.”
Daga nan Minista Idris ya ci gaba da bayyana irin nasarorin ga jami’an tsaro suka samu wajen daƙile matsalar tsaro a wasu jihohin ƙasar nan daban-daban a ‘yan kwanakin nan.
Discussion about this post