Kotu a yankin Kubuwa dake Abuja ta raba aure tsakanin Hafsat Jimoh da mijinta Abubakar Momoh saboda rashin kauna a tsakanin su kwatakwata.
Alkalin Kotun Mohammed Wakili ya ce Hafsat za ta iya yin aure idan ta kammala Iddah.
A zaman da kotun ta yi ranar Laraba Momoh ya bayyana cewa Hafsat ta rufe lambar wayarsa a wayarta inda hakan ya sa baya iya samun ta a waya sannan ta kwashi ‘ya’yan su biyu ta kai su Kaduna.
“Na yi tsawon watanni biyu ba tare da na ga ‘ya’ya na ba duk da cewa na amince da kotu ta raba auren mu sannan duk wata ina aika musu da kudin abinci amma zuwan su kotu yanzu na ga duk sun rame sannan daya daga cikin su na fama da rashin lafiya.
“Mun fara samun matsaloli a ranar da Hafsat ta bi kawarta ta kama gabanta su ka koma wani gidan da zama lokacin da na yi tafiya.
“Tun daga lokacin na yi kokarin ganin iyayen mu sun sassanta mu amma abin ya ci tura.
Hafsat ta ce ita bata hana mijinta gani ko yin magana da ‘ya’yan sa ba.
Ta ce ita ta gaji da auren da babu soyayya a cikinsa da hakan ya sa take so a raba auren su su huta dukkan su kawai.
Discussion about this post