Mazaunan kauyen Jajuwal dake karamar hukumar Toro a jihar Bauchi sun fatattaki ‘yan bindiga yayain da suka kawo musu farmaki a wannan gari na Jajuwul.
Mazauna kauyen Jajuwal tare da hadin guiwar mafarauta da ‘yan banga sun yi batakashi da maharan inda har suka kashe daya daga cikinsu.
Sai dai kuma maharan sun yi garkuwa da wasu mutane a lokacin da suke arcewa cikin daji.
Wani basarake da baya so a fadi sunnan sa bayan ya yabawa kokarin da ‘yan gari suka yi ya ce za su ci gaba da kare kansu daga hare-haren ‘yan bindiga a kauyen.
Zuwa lokacin da aka hada wannan rahoto kakakin rundunar ‘yan sanda jihar bai ce komai ba domin ba a iya samunsa a wayarsa.
Discussion about this post