A ranar Lahadi ne Seyi Tinubu, dan shugaban kasa, Bola Tinubu, ya tashi jirgin shugaban Kasa zuwa Kano domin kallon wasan karshe na gasar Polo.
Jirgin shugaban kasa da ke dauke da Seyi Tinubu da abokansa ya sauka a Kano da tsakar ranar Lahadi. Wasu jami’an fadar shugaban kasa da gwamnatin jihar Kano da wasu ‘yan kungiyar kwallon Polo ne suka tarbe shi a filin jirgin.
Daga nan sai aka zarce da shi zuwa filin wasan kwallon Polo na Usman Danbatta cikin tsaro mai tsanannin gaske da suka hada da jami’an ‘yan sanda, da na SSS.
Bayan an kammala wasan Polon kuma an ba da kyaututtuka, sai jirgin ya kwashe shi da abokan sa zuwa Abuja inda yake zaune.
Sai dai kuma mutane da yawa sun nuna rashin dattaku kan abida ya aikata. Jaafar Jaafar ya saka a shafin sa na X cewa ” Duk da dai a nayi wa dokokin kasar nan katsalandan, ba a daukan su da muhimmanci, Amma dan shugaban kasa ya tashi jirgin shugaban kasa ya don kawai za shi kallon wasan Polo, babau dattaku a cikin sa.
Haka kuma wani a shafin X ya fadi cewa ba kawai zuwa Kano ba, haka kawai zai tafi shakawar sa ko kuma yawaon wasannin sa sai ya jidi lodin jami’an tsaro na ‘Yan sanda da sojoji, ya rika bin shi yana shakatawar sa.
Abin dai bai canja ba
Idan ba a manta ba haka lokacin mulkin Buhari diyar sa Hanan, ta tashi jirgin zuwa Bauchi wai don daukan hoto kawai.
Discussion about this post