Gwamnatin Uba Sani a jihar Kaduna ta dauki nauyin karatun dalibai 50 ‘yan asalin jihar domin karatun kwasakwasan kimiyyar ICT kyauta a Jami’ar Mewar.
Mewar jami’an ce da kasar India ta bude a Afrika ta Yamma kuma Jami’ar ta zama daya daga cikin manyan jami’o’in dake horas da dalibai kwasakwasan ICT da komfuta a Afrika.
A zaman da ta yi da daliban da Iyayen su a dakin taron ‘Sir Kashim Ibrahim House’ mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna Hadiza Balarabe ta yi kira ga daliban da su mai da hankali a karatunsu sannan ta yi addu’a Allah ya kai su lafiya a duk lokacin da suka shirya tafiya jami’ar a jihar Nasarawa.
Jami’ar Mewar ta bada damar daukan dalibai 100 daga jihar Kaduna tare da Bada ƙarfi wajen ganin an fi daukan mata daga cikin yawan da za tura karatu.
An zabo dalibai daga kananan hukumomi 23 kuma wadanda suka yi kokari a jarabawar JAMB inda daga ciki 50 ne aka dauka.
Daga cikin dalibai 50 akwai mata 33 da maza 16.
Discussion about this post