Kotun Ƙoli ta aza ranar Litinin, 23 Ga Oktoba, domin sauraren ƙararrakin da ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, Atiku Abubakar da na LP, Peter Obi suka shigar, inda suka ƙalubalanci nasarar da Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa ta ce Shugaba Bola Tinubu na APC ya yi.
Rajistara ta Kotun Ƙoli, Zainab Garba ce ta bayyana haka a cikin wata sanarwar da ta fitar a ranar Alhamis.
Atiku, Obi da jam’iyyar APM duk sun ƙi amincewa da hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa ta yanke, wanda hakan ya sa duk su ka ɗaukaka ƙara a Kotun Ƙoli.
Su na so Kotun Ƙoli ta soke nasarar da ta bai wa Tinubu a hukuncin da ta yanke a ranar 6 Ga Satumba.
Yayin sauraren ƙarar a wannan makon gobe, Kotun Ƙoli za ta gabatar da Manyan Alƙalai bakwai waɗanda za su bibiyi shari’ar da Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa ta yi, sannan su yanke hukunci.
Lauyan Atiku Chris Uche ya shigar da ƙara kan batutuwa 35. Ya ce Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa ta yi wa Atiku rashin adalci, kuma ta ƙi tsetstsefe dukkan batutuwan da Atiku ya gabatar, maimakon haka, sai aka yi harzarin yanke hukuncin da kotun ta bai wa Tinubu nasara.
Lauya Uche ya ce kotu ta yi amfani da kalmomi na cin mutunci da cin fuska ga Atiku, wanda hakan na nuna kotun ta yi “son kai da ɓangaranci.”
Uche ya ce hukuncin da kotun ta yanke bai kamo hanya ɗaya da irin ƙorafe-ƙorafen da Atiku ya gabatar wa kotun ba.
Akwai kuma ƙorafin cewa INEC ta karya ƙa’idar zaɓe, ta hanyar rashin yin amfani da IReV, a lokacin zaɓen shugaban ƙasa.
A wata sabuwa kuma, Atiku ya shigar da sabbin hujjojin da ya samo na kwafen takardun bayanan Tinubu, daga Jami’ar Chicago ta Amurka.
A ɓangaren Peter Obi, ya shigar da ƙorafe-ƙorafe 51 a Kotun Ƙoli, inda ya ce kwata-kwata Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa ba ta yi masa adalci ba, saɓat-ta-yujat-ta kawai aka yi, ba shari’a ba.
Har yanzu ya na kan bakan sa cewa Tinubu bai yi nasara ba, domin bai samu kashi 25 bisa 100 na ƙuri’un FCT Abuja ba.
Jam’iyyar APM ta garzaya Kotun Ƙoli ne bisa wasu dalilai, ciki har da batun rashin cancantar Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima tsayawa takara.
Discussion about this post