Haramtacciyar kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) ta ce yanzu a shirye ta ke ta tattauna da gwamnatin tarayya kan batun neman ‘yancin yankin Biafra daga Najeriya.
Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ta, Emma Powerful, ta fitar a ranar Asabar, wacce ta kai ha idanun PREMIUM TIMES.
” Mu ƴan kungiyar (IPOB) da ke karkashin jagorancin Onyendu Mazi Nnamdi Kanu muna fatan sake jaddada cewa IPOB kungiya ce mai ƙaunar zaman lafiya sannan burin mu shine gwamnatin Najeriya ta zo mu zauna, a yi yarjejeniya a tsakaninmu, don ficewa daga Najeriya mu kafa kasarmu ta Biafra salin alin.
Powerful ya kara da cewa, suna so a zauna ne ayi rattaba hannu na amincewa tsakanin Najeriya da ƙungiyar. Mutanen yankin kudu maso gabashin Najeriya da wasu daga cikin kudu maso yamma, na son ficewa daga Najeriya.
” Muna so mu kafa ƙasar mu ta Biafra ba tare da an samu matsala ba don mutanen mu mutane ne masu son zaman lafiya.
” Sama da mutum 5000 ne sojojin Najeriya suka kashe. Sun lalata mana kasuwancin mu da gidajen mutanen yankin mu.
Kungiyar IPOB na fafutukar kafa kasar ‘Biafra’ mai cin gashin kai. Burin su shine su fice daga Najeriya su kafa kasar su. Tuni gwamnatin Najeriya ta aiyana ƴan kungiyar a matsayin ƴan ta’adda.
Shugaban su Nnamdi Kanu na nan a tsare har yanzu a kurkukun Najeriya.
Discussion about this post