Rundunar ‘yan sandan jihar Benue ta kama wani magidanci mai suna Bem Matthew mazaunin Korinya-City dake karamar hukumar Konshisha da ake zargin ya kashe matarsa.
Makwabta wanda suka taimaka wajen tsare Matthew zuwa lokacin da ‘yan sandan Konshisha suka zo suka tafi da shi sun ce mijin ya kashe matar sa da misalin karfe 7:03 na safe ranar Talatar makon jiya.
Makwabtan sun ce basu san me ya haɗa su ba amma sun shigo gidan sun iske Matthew tsaye kan matarsa da wuka a hannunsa.
Sun ce Matthew ya daɓa wa matarsa wuka a kirji, baya da kafafuwanta.
A hannun ‘yan sanda Matthew ta tabbatar wa jami’an cewa shine ya kashe matarsa kuma dalilin haka shine don ta daina yi masa biyayya kwatakwata.
Zuwa yanzu Matthew na tsare a ofishin ‘yan sandan sannan gawar matar na asibitin Saint Joseph’s Clinic and Maternity a Korinya City.
Discussion about this post