Jami’an rundunar ‘yan sandan Katsina sun kama wani tsoho mai shekaru 65 da ya yi wa ‘yar shekara hudu fyade.
Kakakin rundunar Abubakar Sadiq ya sanar da haka a makon jiha.
Sadiq ya ce ‘yan sanda sun kama tsohon ranar 7 ga Satumba bayan mahaifin yarinyar ya kawo kara ofishin ‘yan sanda dake Dandagoro.
Ya ce bayan ya shiga hannun ‘yan sanda tsohon ya bayyana wa jami’an tsaron cewa ya danne wannan karamar yarinya a lokacin da je ziyarar gaisuwa ga Iyayen ta a gidan su.
“Ya ce bayan ya isa gidan sai Iyayen yarinyar suka fita suka barshi tare da ‘yar su daga nan shi kuma lallabe ta har ya danne ta.
Sadiq ya ce yan sanda na nan na bincike kan abinda ya faru, nan bada dadewa ba za a gurfanar da tsohon a gaban kuliya.
Discussion about this post