Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi ƙarin haske kan dalilin da ya sa ya umarci sarakuna su mike tsaye lokacin da gwamnan jihar Seyi Makinde zai yi jawabi a wurin taro.
Obasanjo dai na shan suka kan lamarin da ya faru ranar Juma’a a yayin kaddamar da wasu ayyuka guda biyu a garin Iseyin na jihar Oyo, inda tsohon shugaban kasar ya kasance babban bako na musamman.
A cikin wani dan gajeren bidiyo da aka yada a yanar gizo, an ga Obasanjo yana nuna rashin jin dadinsa da yadda sarakunan da ke zaune suka ƙi tashi domin karrama gwamnan jihar, Seyi Makinde, lokacin da zai yi jawabi a wurin taron yana mai cewa sun nuna rashin kunya raini, da kin girmama na gaba.
Da yake magana da harshen Yarbanci, Obasanjo ya umarci sarakuna da ke zauna su tashi su gaida gwamnan jihar Makinde. Cikin rawan jiki Sarakunan sun tashi da sauri suka rusuna suka gaida gwamna Makinde sannan suka zazzauna.
Mutane da dama sun caccaki Obasanjo kan kalaman da ya yi wa sarakunan na umartarsu su da su tashi, inda suka bayyana abin da ya yi a matsayin cin mutuncin al’adun Yarbawa.
Oluwo na Iwo, Abdulrosheed Akanbi, ya yi kakkausar suka ga tsohon shugaban kasar kan abinda ya yi wa sarakunan.
Basarake Akanbi ya ce bai kamata sarakunan su mike tsaye ba lokacin da Obasanjo ya umarce su su mike. Sannan ya kara da cewa lallai Obasanjo ya rubuta wa sarakunan wasikar neman gafara kan rashin mutuncin da ya gurza musu.
“Akwai tsarin mulki kuma akwai al’adu. A tsarin mulkin mu, gwamna shine shugaba a jiha. Dole ne kowa ya girmama shi komai matsayinsa ko shekarunsa. Ya cancanci girmamawa ko da ko matashi ne kuma dole ne a bi dokar kasa.
Obasanjo ya ce wannan shine dalilin da ya sa ya tilasta wa sarakunan lallai su mike tsaye lokacin da gwamna Makinde zai yi jawabi.
Discussion about this post