Jami’an ‘yan sandan jihar Kebbi sun kama harsasai 7,500 da ganyen wiwi da aka yi wa kudi har naira miliyan 600 a cikin wasu motoci biyu.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa daya daga cikin motocin ya taho ne daga kasar Ghana zuwa Togo zuwa Benin sannan ya isa Najeriya. Shi kuma mota ta biyu ya shigo Najeriya ne daga Benin.
Kakakin rundunar SP Nafi’u Abubakar ya sanar da haka da ya ke zantawa da manema labarai a garin Birnin Kebbi.
Abubakar ya ce a ranar 10 ga Satumba da misalin karfe 7:30 na yamma ‘yan sandan dake Saransa-Maje, karamar hukumar Bagudo sun kama babban mota mai lambar rajista IT21520LA da buhunan dauke da kullin ganyen wiwi 4,927 da kudinsa ya kai naira miliyan 300.
Ya ce ‘yan sandan sun kama wasu mutane uku Emmanuel Chukwuma dan asalin jihar Abia, Kanta Bisa dan kasar Ghana da Shola Adeyemi daga jihar Ondo dake da hannu a shigo da wadannan kaya.
“A ranar 12 ga Satumba kuma da misalin karfe 9:30 na yamma ‘yan sanda sun kama mota mai lamba ka,ar haka IT 21608 LA dauke da harsasai a 7,500 da buhuna dauke da kullin ganyen wiwi 4,106.
“Shima a lisafe kudin wiwin zai kai akalla naira miliyan 300.
‘Yan sanda sun kama wani AbdurRasaq Agbola daga kauyen Iyana Ajiya dake Ibadan jihar Oyo dake da hannu da shigo da harsasan da wiwin.
Discussion about this post