Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Gwamna a Jihar Kano, ta shirya za ta yanke hukunci a ranar Laraba, a shari’ar zaɓen gwamna.
A ranar Litinin ce kotun ta bayyana wannan sanarwa ga lauyoyin ɓangarorin biyu.
Ta ce za ta yanke hukunci a ranar Laraba, 20 ga Satumba, a ƙarar da APC ta shigar, inda ta ƙalubalanci nasarar da Abba Kabir Yusuf na NNPP ya samu, a zaɓen ranar 18 Ga Maris.
Tun a ranar 21 Ga Agusta ne dai lauyoyin ɓangarorin biyu suka kammala bayanan su.
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa INEC ta bayyana cewa NNPP ta samu ƙuri’u 1,019,602, inda ta doke APC mai ƙuri’u 890,705.
Abba na NNPP ya tsere wa Nasiru Gawuna na APC da ƙuri’u 128,897.
Sai dai kuma duk da wannan rata, APC ta ƙi amincewa, kuma ta garzaya kotu.
Ƙarar ta ɗauki hankula a ciki da wajen Kano, saboda ana ganin wani yaƙi ne tsakanin manyan ‘yan siyasa na ɓangarori biyu masu adawa da juna, wato Rabi’u Kwankwaso a ɓangaren NNPP da Abdullahi Ganduje a ɓangaren APC.
APC wadda ke da goyon bayan Ganduje ta ce wa kotu an yi zaɓen Kano ba bisa ƙa’idar da Dokar ta 2022 ta gindaya ba.
Lauyan APC Abdul Fagge, ya kira masu gabatar da shaida har mutum 32, kuma ya miƙa wa kotu kwafen takardu daban-daban.
Ciki har da rahoton BVAS na dukkan mazaɓun Jihar Kano.
Baya ga zargin an yi zaɓe ba bisa yadda ya kamata ba, APC ta ce Abba bai cancanci tsayawa takarar gwamna ba.
APC ta ce a lokacin da aka bayyana cewa Abba ne ya ci zaɓe, shi ba ɗan jam’iyyar NNPP ba ne. Ta ce bai cika kwanaki 30 a NNPP ba, domin babu sunan sa a ciki, a cewar lauya Fagge.
Lauyan APC ya kuma gabatar da takardun ƙuri’u fiye da 270,000 da ya ce haramtattu ne aka danƙara wa NNPP.
Dangane da wannan da wasu dalilai ne ya nemi kotu ta bayyana Gawuna na NNPP a matsayin wanda ya yi nasara, ko kuma a maida zaɓen wanda bai kammalu ba.
Shi kuma lauyan NNPP, Bashir Tudun Wazirchi, ya roƙi kotu ta yi watsi da dalilan APC, waɗanda ya ce duk shirme da bankaura ta ke yi.
Ya ce tashin farko dai ba a haɗa da Gawuna wajen shigar da ƙara ba. Don haka tunda wanda ya zo na biyu bai shigar da ƙara ba, APC shirme da ɓata lokaci kaɗai ta ke yi.
Ya ce dukkan zarge-zargen da APC ke yi ba gaskiya ba ce, kuma ta kasa gabatar da hujjoji a kotun.
Ya ce tabbas akwai sunan Abba a cikin rajistar INEC. “Kuma batun mamba na jam’iyya hatta Kotun Ƙoli ta ce magana ce ta cikin jam’iyya. Babu ruwan kotun zaɓe da batun.”
Haka sauran zarge-zargen ya ce APC ta kasa gabatar da shaida ko hujja a kotu.
Tuni dai ɓangarorin biyu su ka duƙufa addu’a.
Discussion about this post