Shugaban Kamfanin BUA, Abdulsamad Rabi’u, ya bayyana cewa nan gaba kaɗan rage farashin buhun siminti, kuma ya na tsare-tsaren ƙara gina masana’antun sarrafa siminti biyu a ƙasar nan.
Rabi’u ya bayyana haka ga manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa, bayan ganawar sa da Shugaba Bola Tinubu, a ranar Juma’a.
Ya ce a ƙarshen watan Disamba zai ƙaddamar da masana’antun biyu, domin taimaka wa wannan gwamnati a ƙoƙarin da ta ke yi na ganin an sauƙaƙa farashin siminti a ƙasar nan.
Ya ce idan aka kafa masana’antun biyu, kamfanin BUA zai riƙa samar da siminti metrik tan miliyan 17 duk shekara kenan.
“Ina godiya da irin karɓar baƙuncin da Shugaba Bola Tinubu ya yi min a yau.
“Na zo Fadar Shugaban Ƙasa, don na shaida masa cewa nan da ƙarshen shekara zan sake gina sabbin masarautu biyu na siminti. Kuma na sanar da shi yadda kasuwancin mu ke tafiya. Sannan na sanar da shi ƙoƙarin da mu ke yi na rage farashin buhun siminti a ƙarshen shekarar nan.”
Abdul Samad ya sanar da manema labarai cewa Shugaba Tinubu ya amince zai je a matsayin babban baƙo na musamman, wanda zai buɗe masana’antun a ƙarshen Disamba, ko kuma farkon watan Janairu.
“Na sanar da Tinubu cewa zan rage kuɗin farashin buhun siminti, daga Naira 5,000 zuwa Naira 3,000 ko Naira 3,500.” Inji Rabi’u.
Discussion about this post