Ƙungiyar CISLAC ta yi kururuwar jawo hankalin ‘yan Najeriya da kuma nuna damuwa, ganin yadda gwamnatin Bola Tinubu ke tseren tsere wa gwamnatin Buhari wajen yawan ciwo basussuka.
Babban Daraktan CISLAC, Auwal Rafsanjani ne ya yi wannan kururuwar a ranar Asabar, cikin wata sanarwar da ya fitar.
Rafsanjani ya nuna matuƙar damuwa ganin yadda bashin da ake bin Najeriya ya ƙaru da kashi 75% bisa 100%, inda yanzu har ya kai ana bin Najeriya bashin Naira tiriliyan 87.
Hakan ya na nufin an samu ƙarin bashin Naira tiriliyan 37.53 kenan, idan aka kwatanta da Naira tiriliyan 49.85 da ake bin Najeriya zuwa ƙarshen Maris, 2023.”
Rafsanjani ya ce wannan gagarimar matsala ce domin halin ƙunci da raɗaɗin tsadar rayuwar da ‘yan Najeriya ke fama da shi, ba zai hana gwamnati ta dakatar da jidalin biyan kuɗaɗen ruwan basussuka a kowane wata ba.
Ya ce hakan na nufin cire tallafin fetur ɗin da aka yi, har gwamnati na ajiye Naira biliyan 400 kowane wata, ba shi da wani tasiri kenan, domin sauƙin da ake tunani dai ba damuwa zai yi ba, ko da a mafarki.
“A daidai lokacin da duniya ke ƙoƙarin ganin an yafe wa wasu ƙasashe wani adadi daga basussukan da ake bin su, ita kuma Najeriya sai zabura ta ke ta na kazar-kazar wajen yawan ciwo wasu basussukan. Lamarin da ake ta yi wa alamar tambaya da mamaki.
Rafanjani ya ce akwai nauyi da haƙƙi a wuyan wannan gwamnati na tashi da magance ƙalubalen da ya dabaibaye ƙasar nan musamman na yawan tulin basussukan da ake bin ta. Sannan kuma ta taka burkin daina ciwo basussukan haka nan.
Ya ce ai masu nazari sun yi ta shawartar gwamnati ta rage facaka da kuɗaɗe, kuma ta rage kashe kuɗaɗe a wajen gudanar da abubuwan da ba su da muhimmanci da kuma daina kashe kuɗaɗe a ɓangarorin da ba su da wani alfanu ga gwamnati da ‘yan Najeriya baki ɗaya.
Ya kuma yi kira ga ‘yan Majalisa cewa su sake tantance yawan basussuka, kuma ba kowace buƙatar ciwo bashi za su yi gaggawar saka hannun amincewa ba, idan Shugaban Ƙasa ya aika masu buƙatar hakan.
Discussion about this post