Dan takarar gwamnan Kaduna na PDP Isah Ashiru ya bayyana cewa lallai yana da yakinin cewa zai yi nasara a kotun sauraren karrarakin zaben gwamnan Kaduna.
A gajeruwar hira da ya yi da PREMIUM TIMES, Ashiru ya ce ” Ina da tabbatacin cewa za mu yi nasara a kotu dake shari’ar zaben gwamnan jihar da muka kai kara.
” Kotu ta saurare mu, Alkalan mu sun mika dukkan korafin mu, ina tabbatar muku da cewa za mu yi nasara InshaAllah a kotu.
” Mutanen Kaduna sun zabe mu, amma aka yi musu murdiya, aka kwace. Za mu karbo musu abinsu a Kotu in Allah ya Yarda.
Tun bayan bayyana Sanata Uba Sani wanda yayi nasara a zaben gwamnan Kaduna, jam’iyyar PDP da dan takarant Ashiru suka garzaya kotu domin kalubalantar zaben. PDP ta ce itace ta yi nasara a zaben sannan ta zargi hukumar zabe da fidda sakamakon zabe biyu a jihar a lokacin.
Bayan haka jam’iyyar ta ce an yi mata murdiya a zaben sannan an lalata mata kuri’u da gangar domin kada ta yi nasara.
Haka ita ma APC da dan takaran ta gwamna Sani, sun bayyana a kotu ta hannun Lauyoyin ta cewa hujjojin da PDP ta bada a zaman kotun maimakon su dulmiyar da ita ce sai kuma ta wanke ta tatas, suka nuna lallai APC da gwamna Sani ne suka yi nasara a zaben gwamnan.
Ana sa ran nan da kwanaki kadan za a yanke hukuncin a kotu. Sai dai kuma zai iya yuwuwa shari’ar ba zai tsaya nan ba sai an dangana da kotunan gaba.
Discussion about this post