Mazauna garin Madada da ke karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara sun ga Daliban Jami’ar Tarayya dake Gusau da ake zargin ‘yan ta’adda ne suka yi garkuwa da su a ranar Talata suna karbar magani a shagunan saida magani a Madada.
Al’ummar Madada na zaune ne a gabar dajin Kuyambana wanda ya ratsa jihohin Kaduna, Neja, Kebbi da Katsina a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa ta tsakiya.
‘Yan ta’addan sun kai hari a wasu dakunan kwanan dalibai mata guda uku a Sabon Gida, da ke wajen garin Gusau, babban birnin jihar Zamfara, inda su ka yi awon gaba da dalibai 24 da wasu mazauna unguwar a ranar Juma’ar da ta gabata.
Sojoji sun ceto dalibai 13 cikin su.
Kauyen Madada na karkashin ikon ‘yan bindiga Ali Kachallah da Dogo Gide. Wannan gari na su ne karkashin ikon su mutane ke rayuwa a wadannan wurare.
Discussion about this post