‘Yan bindiga sun kashe mutum 6 a kauyen Takanai dake masarautar Atiyap dake karamar hukumar Zangon Kataf a jihar Kaduna.
Wannan harin ya auku ne kwanaki biyar biyar bayan ‘yan bindiga sun kashe wata mata kuma suka yi garkuwa da ‘ya’yan ta biyu a Kaura.
Dagacin kauyen Samson Markus ya tabbatar da aukuwar haka wa ‘Punch’ ranar Laraba.
Markus ya ce maharan sun afka kauyen da misalin karfe 7 na daren Talata inda suka kashe mutum hudu ‘yan gida daya sannan da wasu mutum biyu ‘yan gida daya.
Ya ce akwai yara biyu daga cikin mutum shida din da maharan suka kashe.
“Da muka ji rukugin tashin albarusai mun dauka sojoji ne ashe ‘yan bindiga ne suka diro mana daga Zangon Urban.
“Kafin jami’an tsaro su zo maharan sun kashe mutum shida wanda a ciki akwai yara biyu.
“Muna kira ga gwamnati da jami’an tsaro da su kara kokari wajen samar da tsaro a Kudancin Kaduna.
Discussion about this post