Gwamnan Kano Abba Yusuf ya naɗa mutum 44 a matsayin hadimansa wadanda za su yi aiki a ɓangaren hada rahoto, da kuma tallata shi ada ayyukansa a shafukan sada zumunta
Waɗannan hadimai na daga cikin mutum 196 da gwamnan ya naɗa a matsayin masu taimaka masa.
Mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature, ya sanar da ƙarin mutum 115 da za su yi aiki tare da gwamnan ranar Asabar.
Mutum 14 daga cikin waɗanda aka naɗa za su yi aiki a matsayin mataimaka na musamman, 57 manyan mataimaka, 44 kuma “a matsayin ‘yan gwagwarmaya a shafukan sada zumunta” da kuma masu rahoto na musamman.
Gwamnoni da dama suna ta naɗenaɗen hadimai domin cimma burin su da tattabar da sun yi nasara a aikin da suka sa a gaba na cika alkawarin da suka dauka wa mutanen jihar su
Discussion about this post