Rahoton Kwamitin Bincike ya tabbatar da yadda ƙiri-ƙiri Jami’an Kwamitin Aikin Hajjin 2023 na Jihar Zamfara su ka ƙyale wasu sanannun ‘yan bindiga zuwa aikin Hajjin da ya gabata.
Gwamnatin Zamfara ce ta fitar da rahoton, bayan an yi bincike.
Rahoton ya kuma kama wasu jami’an aikin Hajjin na Zamfara da laifin dagargazar kuɗaɗe, rashin rajistar wasu sunayen Maniyyata, zaftare kuɗaɗen alawus na Mahajjata da sauran laifukan harƙallar kuɗaɗe masu yawa.
An fitar da rahoton makonni biyar bayan PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda jami’an tsaro su ka ‘yan bindiga, matan su da wasu ‘infoma’ bayan sun sauka a filin jirgin saman Sultan Abubakar lll, bayan dawowar su daga Hajji.
Kwamitin Bincike ya miƙa wa Gwamna Dauda Lawan rahoton sa a ranar Alhamis, inda a ciki ya bada shawarar a yi gagarumin garambawul a Hukumar Alhajan Jihar. Wani jami’in ne ya shaida haka.
Shugaban Kwamitin, Musa Mallaha, dai an ce ya shaida wa Gwamna Dauda Lawal cewa baya ta ƙyale ‘yan bindiga da iyalan su tafiya aikin Hajji, jami’an Hukumar Alhazai ta Zamfara sun kuma riƙa datsar maƙudan kuɗaɗen gwamnati da na Mahajjata.
“Kuma ba a tantance mahajjata yadda ya kamata ba. An ƙyale ‘yan bindiga sun yi aikin Hajji, an riƙa zaftare wa mahajjata kuɗaɗen alawus ɗin su. Kuma sun yi amfani da asusun ajiyar kuɗaɗe masu yawa, lamarin da ya janyo damalmala lissafin kuɗaɗe da gangan.
“Lokacin da ya ke karɓar rahoton, Gwamna Dauda Lawal ya nuna ɓacin rai dangane da wannan badaƙala da wasu jami’an Hukumar Alhazai ta Zamfara su ka yi.” Haka Kakakin Yaɗa Labaran Gwamna Lawal, Sulaiman Idris ya shaida wa PREMIUM TIMES.
Aƙalla mutum 3102 ne su ka je aikin Hajji daga Jihar Zamfara a 2023.
Gwamna Lawal ya sha alwashin cewa nan da kwanaki kaɗan zai ɗauki matakin da ya dace ya ɗauka ga dukkan masu hannu a wannan ɓarusa.
Discussion about this post