Gwamnan Jigawa Umar Namadi ya tallafa wa mata 1000 ƴan jihar da jarin N50,000 don fara sana’o’i da kuma dogaro da kai.
Shirin karfafawar, a karkashin Ma’aikatar Mata da Walwalar Al’umma da hadin gwiwar Hukumar Tallafi da Samawa Matasa Aiki, ya gudana ne a dakin taro na Ahmadu Bello da ke Sakatariyar Jiha a Dutse.
Da take jawabi a wurin taron kwamishinar mata, Hadiza Abdulwahab, ta yabi Gwamna Namadi bisa tsarin wanda daya daga cikin alkawuran da ya dauka ne yayin neman zabe da kudurori 12 na gwamnatinsa.
Kwamishinar ta gargadi matan da su yi amfani da kudin ta hanyar da ta dace domin cimma manufar gwamnati na rage talauci da karuwar arziki.
“Da farko, mun dauki mutane 150 ne, amma bayan gabatar da sunayen ga gwamna sai yace ‘150 sun yi kaɗan, ya umarci a kara yawan su su kai akalla mata 1000.
“Da haka ubanmu, gwamna, ya kara adadin mata da za su amfana da shirin. Ina gargadi da ku yi amfani da wannan kudin yadda ya kamata.”
Da yake jaddada matsayar gwamnatinsa, gwamna Namadi yace wannan shirin karfafawar gwaji ne wanda zai zama ma’auni ga manya-manyan da za su biyo baya don yakar matsanancin talauci ga mata da matasa.
“Ina mai tabbatar muku da cewa a zagayen shiri na gaba, za mu kara adadin waɗanda za su anfana zuwa mata 5000.
Waɗanda suka halarci taron sun hada da Mataimakin Gwamna, Aminu Usman; Sakataren Gwamnati, Bala Ibrahim; Sakataren Hukumar Samarwa Matasa Sana’a, Habib Ubale; Matar Gwamna, Hadiza Namadi, wacce ta samu wakilcin matar Mataimakin Gwamna.
Discussion about this post