Kwana ɗaya bayan Gwamnatin Tarayya ta bada sanarwar janye tuhumar mallakar bindiga da ta ke yi wa tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, yanzu kuma za ta sake gurfanar da shi domin kotu ta ƙwato Naira biliyan 6.9 hannun sa.
A ranar Laraba ce Ma’aikatar Harkokin Shari’a ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa za ta gurfanar da Emefiele a Babbar Kotun Tarayya da ke Maitama, Abuja.
Shari’ar mallakar bindiga dai wadda aka janye a ranar Talata, a Babbar Kotun Tarayya ta Legas aka fara ta.
Daraktan Shigar da Ƙararrakin Gwamnatin Tarayya na Ma’aikatar Harkokin Shari’a, Abubakar Mohammed, ya shaida wa Mai Shari’a Nicholas Oweibo cewa an janye waccan ƙarar, saboda ana ƙara bankaɗo waɗansu ‘aika-aikar’ da ake zargin Emefiele ya tafka.
Mohammed ya shaida wa manema labarai bayan fitowa daga kotu cewa a yanzu kuma ana cajin Emefiele da zargin aikata laifuka 20.
Emefiele dai na tsare a hannun SSS tun a ranar 10 Ga Yuni.
Daga cikin zarge-zargen da ake yi masa, akwai haɗa baki da ya yi wajen wata harƙalla da kuma zamba wajen fitar da wasu maƙudan kuɗaɗen kwangila.
Za a gurfanar da shi tare da wata ma’aikaciyar CBN mai suna Sa’adatu Yaro, da kuma da kuma kamfanin ta mai suna APRIL 1616 Investment Limited.
Ana zargin Emefiele ya haɗa harƙallar sayo motoci dalla-dalla na Naira biliyan 6.9, shi da Sa’adatu Yaro, a ƙarƙashin kamfanin ta.
CIkin taɓargazar da ake zargin Emefiele ya aikata shi da Sa’adatu Yaro, har da kashe Naira biliyan 1 da Naira miliyan 85.7 wajen sayo mota Hilux guda 47, a cikin 2018.
Sai muka ƙirar Marsandi 10 da aka sayo a kan Naira biliyan 2.2.
Tuni dai har Gwamnatin Tarayya ta bayyana mutane bakwai masu bayar da shaidar wannan harƙalla da ake zargin Emefiele ya aikata.
Cikin waɗanda za su bayar da shaida, har da Daraktan Apex Bank, Stanley Alvan, da wani ma’aikacin bankin mai suna Mike Agboro da kuma Tahir Jafar.
Discussion about this post