Gwamnan Kaduna Uba Sani ya ba iyalan mutum 8 da suka rasu a hadarin ruftawar masallacin Zariya.
Gwamnan ya yi tattaki na musamman zuwa Zariya inda ya garzaya kai tsaye zuwa fadar mai martaba sarkin Zazzau domin yi masa ta’aziyyar rasuwar masallata da aka yi a wannan masallaci.
Haka kuma gwamna Sani, ya ba wadanda ke kwance a asibiti naira 500,000, yayin da waɗanda aka sallama kuma za a basu naira 200,000 kowannen su.
” Ba ma kasar ranar da abun ya auku, amma na turo sakataren gwamnati kafin ni inzo da kai na.
” Za mu zau na mu duba yadda za a sake gina masallacin yadda ba za a sake samun matsala irin haka ba.
Da yake jawabi Sarkin Zazzau, Mai martaba Ahmed Bamalli, ya ce mutum 25 suka afka cikin wannan tsautsayi, amma kuma baya ga wadanda suka rasu, wadanda suka ji rauni na samu kula asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello.
Discussion about this post