Hukumar Kwastam ta kasa ta datse iyakar Najeriya da Nijar da yammacin Juma’a.
Shugaban hukumar ya ce hakan ya biyo bayan umarni ne da shugaban kasa ya bada na a rufe iyakar saboda taurin kai da sojojin da suka yi juyin mulki suka yi na kin sauraren kungiyar ECOWAS.
Kungiyar ECOWAS ta umarci sojijin su maida mulki hannun zaɓaɓɓen shugaban kasar, Mohammed Bazoum.
Zuwa yanzu dai an motocin kaya cike makil na tsaye a iyakokin kasashen biyu, babu shiga ba fita, saboda wannan sabon doka da aka kakaba.
Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya, Adamu Lamuwa, ya tabbatar da cewa Najeriya ba za ta yi amfani da ƙarfin soja kan sojojin mulkin Nijar ba, har sai ta kasance babu wata makawa sai an yi yaƙin sannan za su sauka su bayar da mulkin.
“Amfani da ƙarfin soja a rikicin Nijar shi ne mataki na ƙarshe, bayan an bi dukkan wasu matakan sasanci sun faskara. Kuma ina fatan lamarin ba zai kai ga gwabza yaƙin ba.” Cewar Lamuwa.
Ya bayyana haka a ranar Juma’a, yayin da ya ke wa jami’an diflomasiyyar ƙasashe masu ofishin jakadanci jawabi a Abuja.
Biyo bayan tsamin da dangantaka ta yi tsakanin ECOWAS da Nijar, ƙungiyar ta gayyaci Hafsan Hafsoshin Tsaron ƙasashen su yi taron gaggawa.
Sun fara taro a ranar Laraba, wanda ake sa ran kammalawa a yau Juma’a.
Najeriya ce a matsayin ta na babbar ƙasar da ta fi ƙarfin tattalin arziki a Afrika da ECOWAS, har ma da yawan sojoji, za ta fi bayar da gudunmawar zaratan sojojin da za su yi artabu a Nijar.
Sai dai kuma da aka tambayi Lamuwa ko da gaske ne Nijar ta kori Jakadan Najeriya da ke ƙasar, sai ya ce shi dai har yanzu ba a sanar da shi da baki ko a rubuce ba.
A Najeriya, Shugaba Bola Tinubu wanda shi ne Shugaban ECOWAS, ya rubuta wa Majalisar Dattawa sanarwar shirin afka wa Nijar da yaƙi, don ƙwatar wa Bazoum mulki daga hannun sojoji.
Yayin da Najeriya ke tsakiyar fama da ‘yan bindiga a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, sai kuma Boko Haram, Shugaba Bola Tinubu ya rubuta wa Majalisar Dattawa wasiƙar sanar da su matakan da ECOWAS ta ɗauka domin tabbatar da an dawo da mulkin farar hula a Jamhuriyar Nijar.
Cikin wasiƙar wadda ke ɗauke da sanarwar takunkumin da ECOWAS ta ƙaƙaba wa Nijar, waɗanda har wasu sun fara aiki, har da shirye-shiryen ɗaukar matakin yin amfani da ƙarfin soja, domin a ƙwatar wa hamɓararren shugaban ƙasar, Mohammed Bazoum mulkin sa daga hannun sojoji.
Discussion about this post