Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta kama wani dattijo mai shekaru 77, Adedamola Idowu, bisa zarginsa da yi wa diyarsa ‘yar shekara bakwai fyade.
Shi ma makwabcin Idowu, mai shekaru 26, Oluwatobi Adebisi, an kama shi da aikata irin wannan laifin.
Rundunar ‘yan sandan ta ce an kama mutanen biyu ne a ranar Juma’a a Ijagun, cikin Ijebu-Ode.
Kwamishinan ‘yan sanda, Abiodun Alamutu, ya gabatar da wadanda ake zargin a hedikwatar ‘yan sandan jihar da ke Eleweran, Abeokuta, a ranar Talata.
“Wannan lalataccen dattijo wanda kakan wannan yarinya ne da makwabcinsa sun rika yin lalata da wannan ‘yar karamar yarinya mai shekara bakwai dukkan ba tare da an taba kama su ba sai yanzu.
‘Yan sandan jihar sun kama su kuma tuni an tura cibiya domin a duba kwakwalwan su da kuma ci gaba da bincike akan wannan mummunar abu da suka aikata.
Bayan haka kuma, rundunar ya ya yi wa masu kungiyoyin asiri dake aikata ta’addanci a fadin jihar su shiga taitayin su tun da wuri. Yana mai cewa gwamnati za ta ci gaba da farautar su adaya bayan daya tana hukunta su.
Discussion about this post