A ranar Larabar mai shari’a Dairus Khobo na babbar kotun jihar Kaduna ya yankewa wani mutum Mustapha Saminu mai shekaru 45 hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari bisa samunsa da laifin badakalar naira miliyan 5.
Alkalin wanda bai baiwa wanda aka yanke wa laifin zabin biyan tara ba, ya yanke lallai zai yi biyayya da hukuncin kotu kamar yadda ta yanke.
Ya kara da cewa idan mai laifin ya gaza biyan kudin, zai kara zaman shekara daya a gidan yari.
Tun da farko dai lauyan masu shigar da kara na EFCC, E. K. Garba, ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhuma ya damfari wanda ya kai karar da cewa zai taimaka wa ‘ya’yansa biyu su samu aikin Soja.
Garba ya ce bayan ya karbi har naira miliyan 5daga hannun sa, ya yaudari ‘ya’yan mai korafin zuwa Kaduna wai don su gana da wani jami’i da zai ba su aikin a Zariya.
Da suka is a Zariya sai suka gane ashe dai zamba ce kawai, yaudarar su ya yi. Ya cin ye musu kudi.
Yanzu dai kotu ta umarce shi da ya maida wa Garba naira miliyan 5 din da ya karba.
Discussion about this post