Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC ta bayyana wa Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa cewa ɗan takarar LP, Peter Obi ya kasa gabatar wa kotu yadda ya samu ƙuri’u masu yawan da ya ce sun fi na sauran ‘yan takara.
A cikin bayanan ta na ƙarshe ga kotu, INEC ta ce “zarge-zargen da Peter Obi ya yi, ba su da makama, ƙadda-ƙanzon-kurege ne.”
Lauyan INEC, Abbakar Mahmud, Kashim Shettima ya aika wa INEC sanarwar fasa takarar sanata, a ranar 6 Ga Yuli, 2022, kuma ta samu saƙon a ranar 13 ga wata, 2022.
INEC ta ce “kuma babu wani abin dogaro da za a yarda da shi cewa an taɓa gurfanar da Bola Tinubu a America, har an ci shi tarar kuɗaɗe masu yawa.”
Ta ce zargin tarar da aka ce Bola Tinubu ya bayar a Amirka, ba a saka ta a rekod ɗin kasar a cikin nan ba.
Ya ce batun ƙwace wa Bola Tinubu kuɗaɗe a America, ya zarce shekara 20 da faruwar lamarin.
Don haka ya roƙi kotu ta yi watsi da bukatar Peter Obi.
Shi ma lauyan Bola Tinubu ya ce, “masu cewa a soke zaɓe don bai samu kashi 25% a FCT Abuja ba, molon-ka ne.”
Shugaba Bola Tinubu ya bayyana wa Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa cewa soke zaɓe don ba shi samu kashi 25% a FCT Abuja ba, molon-ka ne.
Ya bayyana haka a cikin rubutaccen ba’asi da ya yi na ƙarshe a shari’ar sa da Peter Obi na LP.
Ya ce FCT Abuja daidai ce da sauran jihohi, saboda haka batun soke zaɓe bata lokaci ne.
Peter Obi na LP ya garzaya kotu ya nemi kotu ta soke zaɓen Shugaban Ƙasa, saboda Bola Tinubu ya rasa samun 25% a FCT Abuja, da wasu dalilai.
Doka ta ce wanda ya yi nasara ya zama ya samu ƙuri’u ɗaya bisa ga uku na wasu jihohi, har da FCT Abuja.
Amma shi Obi ya ce tsarin mulkin Najeriya cewa ya yi tilas sai da FCT Abuja.
A bayanan Bola Tinubu da Wole
Olanipekun lauyan Bola Tinubu ya gabatar, ya ce 25% a FCT Abuja ba dole ba ce.
Ya bayar da Sashe na 134 2b, ya ce a sashen babu wani wuri da aka ce lallai sai da FCT Abuja.
Shi ma ɗan takarar PDP, Abubakar ya garzaya kotu, ya nemi a soke zaɓen.
Discussion about this post