Gwamnan Kaduna, Uba Sani a ranar Talata ya gana da Jakadan Kasar Kuwait a Nijeriya, Abdul’aziz Albisher a kokarin da yake yi na ci gaba da kawo wa Jihar Kaduna cigaba ta hanyar kulla kawance da hukumomin raya kasa.
Albisher ya nuna sha’awarsa na ganin Jihar Kaduna ta kasance jihar da za ta ci gajiyar tallafi daga kasar Kuwait a Najeriya.
Wannan zaman dai ya biyo bayan wata ganawa ce da Gwamna Sani ya yi da Jakadan na Kuwai a ranar Juma’a 9 ga watan Yuni 2023.
Tun bayaan ɗarewar sa kujerar gwamnan Kaduna gwamna Sani ya gana da jakadu da manya jami’an gwamnatin Najeriya inda suka tattauna don lalubo hanyar da za a samu ci gaba a musamman jihar Kaduna.
A kwanakin baya, gwamnan ya gana da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaron Kasa Nuhu Ribaɗu, da hafsoshin tsaron kasa.
A gawar gwamna Sani ya jawo hankulan su gaba daya kan game da matsalar tsaro da yadda za a shawo kan matsalar a jihar.
Discussion about this post