‘Yan sanda a ranar Talata sun kai karar wata mata mai suna Linda Shedrach mai shekara 35 kotun majistare bayan an kamata da laifin sace gashin da ake kara wa mata a akai na naira 82,000.
Linda mazauniyar Unguwan Maigero ne a Kaduna.
Dan sandan da ya shigar da karar Samson Ejiofor ya ce wata Helen Williams dake zama a Unguwar Narayi ne ta Kai karar satan da Linda ta yi a ofishin ‘yan sandan dake Barnawa ranar 10 ga Yuni.
Ejiofor ya ce Helen ta bayyana wa jami’an tsaro cewa Linda ta shiga shagonta dake Narayi Bus stop ta saci gashin naira 82,000.
“Helen ta gane cewa yawan gashin dake shagon sun yi matuƙar raguwa bayan Linda ta fice.
“Nan da nan Helen ta yi ihun barauniya sai Lunda ta jefar da jakan da ta saka kashin ta fece. Ko da aka duba jakar sai aka ga tarin gashin.
A kotun Linda ta musanta zargin sarar da ake mata.
Alkalin kotun Dauda Solomon ya Bada belin Linda akan naira 150,000 tare da gabatar da shaida daya a gaban kotun.
Solomon ya ce shaidan da Linda za ta gabatar zai gabatar da shaidan cewa yana aiki sannan yana biyan haraji wa gwamnatin jihar Kaduna na tsawon shekaru biyu.
Ya ce za a ci gaba da shari’a ranar 12 ga Yuli.
Discussion about this post