A ci gaba da kula da ma’aikatan sa da yake yi a koda yaushe Farfesa Adamu Gwarzo ya yi wa wani tsohon ma’aikacin jami’ar mai kula da shige da ficen mutane a makarantun, da ke Nijar da Najeriya, Umar Sanda kyautar gidan zama sukutum.
Farfesa Gwarzo ya ya mika wa Sanda mukullen wannan gida a wata gajeruwar bikinwanda aka yi a ofishinsa ranar Laraba.
A jawabin da ya yi a lokacin mika wa Sanda mukullan Farfesa Gwarzo ya hori sauran ma’aikatan jami’an su maida hankali matuka wajen aiki tukuru domin samun yarda da aminci irin wanda Samda ya nuna har aka kai ga yi masa irin wannan kyauta.
” Sanda ya nuna kwarewa da hakuri matuka a aikin sa. Abinda ka ce yayi, shi ne ya ke yi ba ya saba maka komai tsaurin abu.
” Ya yi mana aiki a Nijar da Najeriya, duka jami’o’in biyu kuma ya nuna kwarewa da biyayya.
Na yi masa wannan kyauta domin ya samu matsuguni da shi da iyalan sa.
Baya ga wannan kyauta da aka yi wa Sanda, Farfesa Gwarzo ya sa an kara masa girma a wurin aiki.
Farfesa Adamu Gwarzo mutum ne da mutane da dama ba su yi masa kirari da babu irin sa cikin mutane musamman a wannan lokaci da muke cike a kasar nan.
A duk lokacin da za ka ambaci sunan sa to sai ka ji an yaba masa kan wani abu na taimako da ya yi.
Discussion about this post