Gamayyar zaɓaɓɓun sanatocin yankin Arewa ta Tsakiya, sun bayyana Sanata Sani Musa cewa shi su ke so ya zama Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa daga 2023 zuwa 2027.
Zaɓaɓɓun Sanatocin daga Neja, Benuwai, Filato, Nasarawa, Kogi da Kwara sun ce idan aka yi masu haka, to an raba romon dimokraɗiyya tare da yankin su kenan.
Zaɓaɓɓen Sanatan Nasarawa ta Yamma, Aliyu Wadada ne ya bayyana wannan matsaya ta su, lokacin da ya yi wa manema labarai bayani, bayan tashin su taro sanin makamar aikin da aka ƙaddamar wa zaɓaɓɓun ‘yan majalisa, a Abuja.
Wadada wanda aka zaɓa a ƙarƙashin SDP, ya ce ya na tattaunawa shi da sauran sanatocin da aka zaɓa daga yankin, domin su samu mataimakin shugaban majalisar dattawa.
Ya ce hakan kuwa su na yi ne duk da bambance-bambancen siyasar da su ka fito.
Wadada ya fitar da wannan matsaya ta su, jim kaɗan bayan shi da ɗaya sanata daga Nasarawa, Godiya Akwashiki, sun bayyana goyon bayan su ga Sanata Godswill Akpabio ya zama Shugaban Majalisar Dattawa.
Kenan ɗaya matsayar ta su na nufin ba su amince a bai wa Barau Jibrin Sanatan Kano mataimakin shugaban majalisar dattawa ba.
Duk da cewa a bayan kafafen yaɗa labarai sun bayyana cewa Wadada ya goyi bayan Barau Jibrin ya zama mataimakin shugaban majalisar dattawa, yanzu daga baya ya ce jaridu ba su ruwaici abin ya ce daidai ba kan Barau.
Wadada ya ce matsayar sa ita ce, don ya amince da Godswill Akpabio wanda Tinubu ke so, hakan ba ya na nufin shi Wadada ɗin ya amince da Barau Jibrin ba.
“Ba fa za mu yarda a yi rabon muƙamai haka kawai a manta da yankin Arewa ta Tsakiya ba.
“In dai yankin mu na da jajirtattun wakilai a majalisa irin mu, to za mu yi iyakar ƙoƙarin mu domin ganin mun ƙwato wa yankin mu haƙƙin da ya cancanta da wanda ya wajaba a ba shi.” Inji Wadada.
Discussion about this post