Sufeto Janar Usman Alƙali ya kammala nazari da binciken fayil ɗin bayanan zargin kisan ‘yan adawa da ake wa Alhassan Doguwa, Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Tarayya, kuma Ɗan Majalisa mai wakiltar Ƙananan Hukumomin Tudun Wada da Doguwa na Jihar Kano.
Tuni dai Alƙali ya maida wa Gwamnatin Jihar Kano fayil ɗin domin a gurfanar da Doguwa a gaban alƙali.
Tun da farko dai ‘yan sanda ne a Kano su ka kama Doguwa, inda su ka maka shi Kotun Majistare, bisa zargin sa da kisan mutane uku a ranar 25 ga Fabrairu, ranar zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisar tarayya.
Rikici ne ya afku tsakanin magoya bayan APC, jam’iyyar Doguwa da magoya bayan NNPP, wanda ya yi sanadiyyar ƙone magoya bayan NNPP uku a cikin ofishin jam’iyyar su, cikin garin Tudun Wada, mazaɓar da Doguwa ke wakilci a Jihar Kano.
An maida shari’a Babbar Kotun Tarayya, inda ta bada belin sa a kan kuɗi naira miliyan 500.
Sai dai kuma Doguwa ya zargi Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano, Husseini Gumel da yi masa rashin adalci da nuna masa ɓangaranci yayin da ya ke binciken rikicin.
Doguwa ne ya nemi hedikwatar ‘yan sanda ta Abuja ta karɓi binciken da kan ta.
Tawagar binciken Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, waɗanda su ka karɓi fayil ɗin daga Kano, sun aika da sakamakon da su ka gano a Antoni Janar kuma Kwamishinan Shari’a na Kano, Mai Shari’a Musa Lawan, a ranar Juma’a.
Yanzu abin da ya rage shi ne gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da Doguwa a tuhume shi da zargin tafka babban laifi.
Kwamishina Lawan ya ce ma’aikatar sa ta shari’a za ta yi nazarin fayil ɗin da Sufeto Janar ya aika mata, daga nan za ta ɗauki matakin da ya dace na gaba, a cikin makonni biyu.
A ranar 29 Ga Mayu ne mulkin Gwamna Abdullahi Ganduje zai ƙare, wanda hakan na nufin kafin a gurfanar da Doguwa, sai zamanin mulkin Zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf kenan.