A ranar Juma’a ce Kotun Ɗaukaka Ƙara a Abuja ta ɗage sauraren ƙarar da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na HDP a zaɓen 2019 ya maka Bola Tinubu, inda ya nemi kada kotu ta rantsar da shi saboda wasu dalilai.
An ɗage sauraren ƙarar wadda Ambrose Owuru ya shigar, inda ya yi iƙirarin cewa an yi masa rashin adalcin hana shi nasarar da ya yi a zaɓen 2019, aka bai wa Buhari.
Don haka ne a yanzu Ambrose Owuru ya nemi a rantsar da shi ya yi zangon sa na 2019 da aka ba Buhari.
Ambrose Owuru dai ya sha fitowa zaɓen shugaban ƙasa, amma bai fito a zaɓen 2023 ba.
An ɗage sauraren ƙarar da ya shigar ana saura kwanaki 10 a rantsar da Tinubu, lamarin da ke nuni da cewa akwai tabbacin rantsar da Tinubu ɗin kenan a ranar 29 Ga Mayu.
Alƙalan Kotun Ɗaukaka Ƙara su uku bisa jagorancin Jamil Tukur, sun ɗage ƙarar har sai ranar da su ka ce za su sanar da ɓangarorin biyu na mai ƙara da wanda ake ƙara ranar da za a koma kotu.
Dalilin Ambrose Owuru Garzayawa Kotu Neman A Rantsar Da Shi, Ba Tinubu Ba:
Tsohon ɗan takara ya nemi kotu ta haramta nasarar Buhari a 2019, a rantsar da shi maimakon Tinubu a 29 Ga Mayu.
Tsohon ɗan takarar jam’iyyar HDP a zaɓen shugaban ƙasa, Ambrose Owuru, ya nemi Kotun Ɗaukaka Ƙara kada ta bari a rantsar da Bola Tinubu matsayin shugaban ƙasa a ranar 29 Ga Mayu.
Wannan ƙara da Ambrose na HDP ya shigar, ita ce ƙara ta shida da jam’iyyu da ‘yan takara daban-daban su ka shigar su na nuna rashin amincewa da nasarar Bola Tinubu na APC.
Sai dai su waɗancan biyar ɗin, sun maka Bola Tinubu ƙara ce a Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa, shi kuwa Ambrose a Kotun Ɗaukaka Ƙara ya kai ta sa ƙarar.
Daga cikin waɗanda su ka maka Tinubu ƙara kotu, akwai PDP da Atiku Abubakar, LP da Peter Obi.
A ƙara mai lamba CA/CV/259/2023 wadda Ambrose ya shigar, ya nemi a dakatar da rantsar da Bola Tinubu. Kuma a cikin waɗanda ya ke ƙara, ya haɗa har da Shugaba Muhammadu Buhari da Antoni Janar Abubakar Malami da kuma Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC).
Ambrose Owuru wanda lauya ne, ya yi takara tun a zaɓen 2019 a ƙarƙashin HDP, kuma ya sha kaye a hannun Buhari, amma sai ya yi iƙirarin cewa shi ne ya yi nasara.
A kan haka ne Ambrose Owuru ya haƙiƙice cewa shi ne ya yi nasara, amma aka ba Buhari.
Don haka ya ce wa kotu Tinubu ba zai yiwu ya zama shugaban ƙasa ba a 2023, har sai an rantsar da shi Ambrose ɗin ya yi shekaru huɗu na zangon sa tukunna.
Hujjar Da Ambrose Owuru Ke Taƙama Da Ita:
Ya ce, “Shugabancin Muhammadu Buhari na 2019 zuwa 2023 haramtacce ne, domin an rantsar da shi alhali Kotun Ƙoli ba ta yanke hukuncin ƙarar Buhari da ya shigar kan zaɓen Buhari ba.
Saboda haka ya nemi kotu ta hana “miƙa mulki daga hannun Buhari zuwa hannun Bola Tinubu a ranar 29 Ga Mayu. Sannan kuma ta hana rantsar da Tinubu ɗin, saboda Kotun Ƙoli ba ya yanke hukuncin ƙarar zaɓen Buhari da ya kai tun cikin 2019 ba.”
Lauyan Ambrose Owuru mai suna Odion Peter, ya roƙi Kotun Ɗaukaka Ƙara ta gaggauta yanke hukuncin ƙarar da ya shigar kafin ranar rantsarwa.
Discussion about this post