Kotun sauraren kararrakin zaben shugaban kasa da ke Abuja a ranar Larabar ta yi watsi da wata karar da jam’iyyar Action Peoples Party (APP) ta shigar da take ƙalubalantar nasarar Bola Tinubu a matsayin zababben shugaban Najeriya.
Idan ba manta ba, a ranar Litinin kwamitin Alƙalai biyar na kotun karkashin jagorancin Haruna Tsammani suka yi watsi da karar da jam’iyyar Action Alliance (AA) ta shigar biyo bayan janye karar da jam’iyyar ta yi kan nasarar da Tinubu ya samu.
Tinubu wanda ya tsaya takarar shugaban kasa a zaben shugaban kasa na ranar 25 ga Faburairu karkashin jam’iyyar APC, na fuskantar kararraki biyar da ke kalubalantar nasarar da ya yi.
Wadanda suka shigar da karar sun hada da jam’iyyun siyasa da ‘yan takararsu da suka hada da Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da Peter Obi na jam’iyyar Labour. Dukkan su sun gabatar da kokensu kan yadda Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta gudanar da zaben ne.
Sun bukaci kotu da ta soke nasarar Tinubu tare da ba da umarnin sake gudanar da zabe.
Sai dai kuma a ranar Laraba lauyan dake kare jam’iyyar APP, Obed Agu, ya bayyana wa alƙalai a kotu cewa jam’iyyar ta janye karar da ta shigar kan nasarar da APC ta yi a zaɓen shugaban kasa.
Agu ya ce APP ta rubuta wasikar janye ƙarar a ranar 9 ga Mayu. Sai dai bai bayyana dalilin da ya sa jam’iyyar ta janye korafe korafenta da ta ke yi kan nasarar Tinubu ba.
Discussion about this post