Zaɓaɓɓen shugaban kasa Bola Tinubu ya nausa Turai domin tattaunawa da gaggan kamfanoni da ƴan kasuwa da za su saka jari a Najeriya.
Waɗanda zai gana da su sun haɗa da jugajigan kamfanoni da mu harkar bunƙasa ayyukan noma, kasuwanci da dai sauransu.
Ofishin yaɗa labarai na Tinubu ta sanar cewa bayan haka Tinubu zai cigaba da ganawa da kuma tsara yadda gwamnatin sa za ta kasance da kuma irin mutanen da zai yi aiki da su domin cika alkawarin da yayi na soma aiki gadan-gadan daga ranar da aka rantsar da shi.
” Bunkasa tattalin arzikin kasa na daga cikin muhimman abubuwa da Tinubu zai fi maida hankali a kai. Bayan haka zai bunkasa ayyukan noma ya yi daidai da yadda ake samu a kasashen da suka ci gaba, da kuma jayo masu saka jari domin bunkasa harkokin kasuwanci a Najeriya.
Saura kwana 19 a rantsar da sabuwar gwamnati karkashin zaɓaɓɓen shugaban kasa Bola Tinubu.
A wannan rana ne shugaba Muhammadu Buhari zai yi sallama da fadar Aso Rock, bayan kammala shekaru 8 da yayi a matsayin shugaban kasa daga 2015 – 2023.