Hamshaƙin attajirin ɗan kasuwa Femi Otedola, ya zargi Shugaban Transnational Corporation of Nigeria (Transcorp), Tony Elumelu ya riƙa yi masa yankan-baya ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba.
Elumelu ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya fito fili ya yi bayani a cikin kwafen takardun da su ka gilma ta kan teburin PREMIUM TIMES, ta damƙe.
Kwanan nan ne hamshaƙin attajiri Otedola ya fara gugumarar kokawar fifikon hannun jari da Transcorp Group.
A ɗaukin da Otedola ya kai a ranar Talata, ya bayyana cewa cikin 2008 ya taɓa talaucewa a daidai lokacin kuma Elumelu ya ci amanar sa.
“Na zama Shugaban Transcorp Hotel cikin 2007 ina da kashi 5 bisa 100 na hannayen jarin otal ɗin.
Ni ban sani ba ashe Tony Elumelu ya riƙa sayen hannayen jari a Transcorp ɗin a ɓoye.” Inji Otedola.
“Ai yayin da shekarar 2008 ta zo, harkokin hada-hada ta sun durƙushe a Najeriya. A nan ma sai Tony Elumelu ya garzaya ya saye hannayen jari na a Bankin UBA domin a riƙa biyan kuɗin ruwan bashin da na karɓa. Bai tsaya a nan ba, ya garzaya Africa Finance Corporation, inda a can ma ni na fi kowa yawan hannayen jari.
“Daga nan ba da daɗewa ba, sai Albert Okumagba ya shaida min cewa wani kamfanin Amurka na so ya sayi hannayen jari na a Transcorp, ni kuma na amince zan sayar ɗin.
Ashe ni ban sani ba, kamfanin Amurka ɗin da ake magana ba kowa ba ne sai Tony Elumelu. Haushin wannan cin amana ce da aka yi mani na fusata na sauka daga Shugaban Transcorp Hotel.”
Otedola har ila yau ya ƙara da cewa cikin 2012 ya shaida wa Elumelu buƙatar da ya ke da ita a tashar lantarki ta Ughelli. Sai Elumelu ya ce ba tare da sanin Otedola ba ya kewaya ya sayi tashar wutar lantarkin.
“Har ofis ya same ni ina ganawa da wasu Turawa. Bayan mun kammala na sane shi ya tambaye ni ganawar me mu ka yi? Na ce masa ai tashar lantarki ta Ughelli na ke shawara na saya.
“Ba tare da na sani ba daga nan sai Elumelu ya kewaya ya saye ta a dala miliyan 300.
“Duk sauran batutuwa kuma sun zama tarihi.”
PREMIUM TIMES ta kasa samun Elumelu ballantana ta ji ta bakin sa.
Elumelu a matsayin sa na Shugaban Kamfanin Lantarki na Transcorp, ya samu satifiket daga BPE a ranar Litinin.
An dai ƙaddamar da Tashar Lantarki ta Ughelli tun cikin 1966 da ƙarfin iya samar da wutar lantarki migawat 972. Ta zama kadarar Transcorp Corporation of Nigeria Plc cikin 2013 da suna Transcorp Ughelli Power Limited.
Discussion about this post