Hedikwatan tsaron Najeriya DHQ ta bayyana cewa a cikin makonnin biyu da suka gabata sojin Najeriya sun kashe ‘yan ta’adda 30 sannan sun kama wasu 48 a yankunan Arewa ta Tsakiya da Arewa maso Yamma.
Darektan yada labarai na hedikwatar tsaro Musa Danmadami ya sanar da haka a Abuja ranar Alhamis.
Danmadami ya ce a Arewa ta Tsakiya rundunar ‘Operation Safe Haven’ da wasu jami’an tsaron a wasu kauyukan dake jihohin Benue, Niger, Nasarawa da Filato da Babban Birnin Tarayya Abuja sun kashe ‘yan bindiga 5 sannan sun ceto mutum 10 da aka yi garkuwa da su.
Bayan haka a yankin Arewa maso Yamma Danmadami ya ce rundunar sojin sama da kasa dake aiki a karkashin rundunar ‘Operation Hadarin Daji’ sun kai wa ‘yan bindiga hari a mabuyar su dake jihohin Katsina, Kaduna, Sokoto da Zamfara.
Ya ce a wadannan jihohin sojoji sun kashe ‘yan bindiga 25, sun kama mutanen dake hada baki da mahara 30, mutum shida, mutum biyu masu siyar wa mahara bindigogi da wasu mutane hudu aka yi garkuwa da su.
Danmadami ya ce daga ranar 21 zuwa 25 ga Afrilu dakarun sun kashe ‘ysn bindiga 14 inda a cikin su akwai wani kasurgumin dan bindiga.
Ya ce dakarun sun kama makamai da dama tare da wasu mutane biyu da ake zargin masu safarar muggan kwayoyi ne da aka kama su a kauyen Wazata dake karamar hukumar Birnin Gwari.
“Bincike ya nuna cewa wadannan mutane biyu da aka kama sun dade suna siyar wa yan bindiga makamai da muggan kwayoyi.
“Sojojin sun kama harsasai 15, wayoyi 8, kulin wiwi 105, kwayoyin Tramadol guda 1,032 da kudi Naira 82,800.
A ranar 23 ga Afrilu sojoji sun kama wasu hadimai masu yi wa yan bindiga hidima su uku da babban mota dauke da buhunan shinkafa 87 a kauyukan Gusami da Mada dake kananan hukumomin Birnin Magaji a Gusau.
Binciken da sojojin suka gudanar ya nuna cewa buhunan shinkafan dake cikin motan da aka kama na wani babban dan bindiga ne da jami’an tsaro ke neman sa ruwa a jallo.