Rajistaran Hukumar Rajistan Kwararrun Malamai ta Kasa (TRCN) Josiah Ajiboye ya bayyana cewa kashi 70% na malaman dake koyarwa a makarantu masu zaman kansu ba su da kwarewa.
“Sakamakon binciken da muka gudanar ya nuna cewa mafi yawan malaman dake koyarwa a makarantu masu zaman kansu a kasar nan ba su da kwarewa, wasu ma sam basu cancanta suna koyarwa ba.
Ajiboye ya fadi haka ne a taron saka hannu a takardan yarjejeniya tsakanin TRCN da Kungiyar INSTILL dake kasar Afrika ta Kudu.
Samun malaman da basu da kwarewar koyarwa na cutar da dalibai sannan da tsarin ilimin boko.
“Wadannan malamai basu da rajista da TRCN saboda basu mallakin abin da ya kamata su mallaka domin yin rajista da hukumar ba.
“Saboda gibin da ake da shi na karancin kararrun malamai ya kamata a rika kiran malaman da basu cancanta ba da sunan ‘yan damfara.
Ya ce malaman boko da dama a Najeriya basu da horo irin na zamani sannan suna amfani da tsoffin kayan aiki wajen koyar da yara.
” Duk malamin da ya ke bashi da horo, ya tabbata ɗan damfara ne domin bashi da abinda zai koyar wa yaron da bai san komai ba wanda dashi ya dogara. Idan ba damfara ba to me nene sunan abinda yake yi?
Ajiboye ya ce saka hannu da TRCN ta yi da kungiyar INSTILL hanya ce da zai taimaka wa malaman kasar nan wajen samun horo irin na zamani domin inganta koyarwar da suke yi a duka makarantun kasar nan.