Zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya yi alkawarin kwararawa ma’aikatan jihar Kaduna marka-markan ababen more rayuwa domin jin daɗin su bayan an rantsar dashi a 29 ga Mayu.
Ina taya ma’aikatan Najeriya da kungiyar kwadago murnar zagayowar ranar ma’aikata. Kun bayar da gudunmawar da ba za ta iya misaltuwa ba wajen gina kasa da wadata kasar Najeriya. Sadaukarwar ku na nan a rubuce-rubuce ba za a manta da shi ba har abada.
Al’ummarmu ta sha fama da kalubale. Abin farin ciki ne a lura da cewa ba ku yi kasa a gwiwa ba a kan sadaukar da kai ga ci gaban kasa da ci gaban al’umma. Kun kare dimokuradiyyar mu da yancin jama’ar Najeriya. Kuna tsayawa kan hadin kan kasa a kowane lokaci. Ma’aikatan Najeriya da kuma ’yan kwadago su ne ginshikan ci gaban Najeriya da hadin kan kasa.
A wannan karon da ba a mantawa da shi ba, ina mika godiya ta musamman ga ma’aikatan jihar Kaduna masu kwazo da basira. Kun bada gudunmawarku da jajircewa wajen ganin an samu ci gaba a jihar mu. Gwamnatina za ta yi aiki da ku kafaɗa da kafaɗa. Zan ba da fifiko da maida hankali matuka ga jin daɗin ku da samar muku da kayan aiki da duk abinda za ku bukata don jin dadin ku da kuma samun nasara a aikin ku.
” Ma’aikatan Kaduna za su san ana yi da su yanzu, ma’aikata masu kwazo za su shaida ta hanyar karramasu da basu kyaututtuka, sannan zan tabbatar da jindadin su a koda yaushe.
Discussion about this post