Gwamnatin jihar Kaduna a ranar Asabar ta bayyana cewa ta kama ‘yan kwaya, ‘yan iska, barayin waya da ‘yan sara suka 98 da suka buwayi mutane a jihar a sassan jihar daban daban.
Kwamishinan tsaron jihar Kaduna ya bayyana cewa gwamna Nasir El-Rufai da kansa ne ya bada umarnin lallai a bi lunguna da unguwannin jihar domin kamu wadannan ‘yan iska da suka addabi mutane a wadannan kwanakin.
Aruwan ya ce : Wadannan matasa sukan tare mutane su kwace musu wayoyi da kudaden su. A dalilin haka da yawa sun ji rauni, wasu ma har rayukan su ya salwanta.
Rahotan Kamen da gwamnatin ta samu ya nuna cewa an kama bata gari guda 98 tsakanin ranar 26 zuwa 28 ga Afrilu inda daga cikin su kotu ta yanke wa mutum 19 hukunci yayin da sauran na tsare kafin a yanke musu hukunci.
Aruwan ya ce wasu mutum 18 daga cikin yawan da aka kama an kai file din karansu sashen dake gurfanar da masu aikata laifi na jihar domin ci gaba da gudanar da bincike.
Ya ce an kama batagari da wayoyin sata, wukake,almakashi, gorori, ganyen wiwi, haramtattun kwayoyi da dai sauran su.
“Gwamnan ya yi kira ga mazaunan unguwanin da suka hada da Rigasa, Kawo, Unguwar Muazu, Badarawa, Kwaru, Rigachikun, Barnawa, Ungwan Rimi, Trikania, Nasarawa, Makera, Sabon Tasha, Narayi, Rafin Guza, Tudun Wada da su hada kai da jami’an tsaro wajen ganin sun bada sunayen bata gari irin haka dake unguwanin su.
“Ya ce za a iya samun jami’an tsaro a wadannan lambobin waya kamar haka: 09034000060 da 08170189999 domin kai kara ko korafi.
Discussion about this post