Shugaban Rukunin kamfanonin Dangote Aliko Dangote ya bayyana a yau litinin cewa tacaccen mai daga kamfanin sa daga cikin ganaga 650,000 dduk rana da za arika tace wa zai shiga kasuwannin mai na kasa kuma a fara amafani da shi a cikin watan Yulin wannan shekara.
Dangote ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a lokacin kaddamar da matatar man a garin Legas ranar Litinin.
” Muna sa ran wannan kamfani zai yi aiki da samun nasarori kamar yadda muka samu a harkar Siminti da Takin zama. Wanda a da mune a kan gaba wajen shigo da su daga kasashen waje, amma bayan kafa kamfanonin da maida hankali da muka yi mu ka zama cikin kasashen da ake fita da wadannan kaya zuwa kasashen waje.
Matatar mu zata samar da ingantaccen mai domin masana’antun mu da kuma wadata fannin sufurin kasar nan.
“Mun gina matatar mai mai karfin sarrafa ganga 650,000 a kowace rana shi ne mafi girma a duniya. sannan an gina kamfanin da fasahar zamani da za a iya samu a ko’ina a fadin duniya. Sannan kuma baya ga haka za a iya fita da tataccen man mu zuwa wasu kasashen don siyarwa.
kamfanin mai na Dangote
A yau Litinin Shugaba Mai Barin Gado, Muhammadu Buhari zai buɗe Matatar Fetur ta Ɗangote, a Legas.
Matatar za ta fara aiki, inda a kullum za ta riƙa tace ganga 650,000.
Matatar wadda babu irin ta a Afrika, ana sa ran manyan baƙi da su ka haɗa da Shugaban Togo, Gnassingbe Eysdema, na Senegal Macky Sall, na Jamhuriyar Nijar Mohammed Bazoum da na Chadi Mahamat Deby.
Matatar dai babu kamar ta wajen girma a duniya, za a buɗe ta ne kusan daidai lokacin da Najeriya za ta cire tallafin fetur.
A shekarar 2005 Najeriya ta biya Naira biliyan 351 kuɗin tallafin fetur. A 2022 kuma ta biya har Naira Tiriliyan 4.39. Daga Janairu zuwa Yuni na 2023 kuma lokacin da Gwamnatin Buhari za ta sauka, za a biya kuɗin tallafi har naira tiriliyan 3.6.
Ɗangote ya kashe dala miliyan 19 wajen kafa matatar, wadda ke da ta gina wa kanta tashar samar wa kan ta wutar lantarki har migawatts 435, ta na da tashar jiragen ruwa na ta na kan ta, sannan kuma an kafa masana’antar yin takin zamani a cikin matatar.
Ana sa ran Matatar Ɗangote ta riƙa tace dukkan fetur ɗin da ake buƙata a Najeriya da ƙasashe maƙautan Najeriya.
Matatar za ta riƙa tace gas da dizal na jiragen sama.
Shugabannin Matatar Ɗangote sun ce an kafa matatar daidai da irin tsarin da Bankin Duniya, Amurka da Turai su ka shar’anta a kafa matatar fetur.
Discussion about this post