‘Yan bindiga sun kashe manoma 9 a Unguwar Danko dake kusa da kauyen Dawa a karamar hukumar Birnin Gwari jihar Kaduna.
Kamar yadda jaridar ‘Daily Trust’ ta buga ranar litinin ‘yan bindigan sun dira wa manoman a lokacin da suke aiki a gonakinsu ranar Asabar da rana tsaka.
Wasu mazaunan kauyen sun ce maharan sun yi awon gaba da wasu manoma guda uku.
Zababben Dan majalisar dokoki na jihar dake wakiltan Kakangi, Yahaya Musa Shima ya tabbatar da aukuwar lamarin yana mai cewa wadanda suka ji rauni a dalilin harin na asibiti likitoci na duba su.
“Eh, an tabbatar min da safiyar Lahadin nan cewa ‘yan bindiga sun kashe manoma tara a Unguwar Danko kusa da kauyen Dogon Dawa a ranar Asabar da yamma, wasu kuma suka samu raunuka harbin bindiga.”
A cewarsa, wasu da suka fusata daga cikin mutanen kauyen sun yi gaba da gaba da ‘yan bindigar, lamarin da ya sa wasu mutanen kauyen suka samu raunuka.
Jihar Kaduna na daga cikin jihohin yankin Arewacin Najeriya dake fama da hare-haren ‘yan bindiga. Yankin Birnin Gwari ta yi fama da hare-haren yan binda na tsawon shekaru da dama.
Discussion about this post