Kungiyar likitocin Najeriya NARD za ta fara yajin aikin kwanaki biyar idan har gwamnati bata biya bukatunta ba.
Shugaban kungiyar Emeka Innocent wanda ya sanar da haka ya ce kungiyar ta dauki wannan maraki ne a zaman da ta yi ranar Litini.
Kungiyar ta ce za ta fara yajin aikin da misalin karfe 8 na safiyar Laraba 17 zuwa ranar Litinin 22 na Mayu da misalin karfe 8 na safe.
Idan ba a manta a ranar 29 ga Afrilu kungiyar ta sanar cewa za ta fara yajin aikin makonni biyu idan har gwamnati bata biya bukatunta ba.
A lokacin ministan kwadago Chris Ngige ya kwatanta bukatun na su da suke so gwamnati ta biya musu a matsatin abu na mutanen da basu da hankali.
Ngige ya ce kungiyar likitocin ta dage sai gwamnatin tarayya ta biya duk bukatunsu dole.
“Gwamnati ta yi kokari wajen biyan bukatunsu musamman bukatun da suka hada da biyansu alawus yayin da suke samun horo tare da albashinsu ko da basu aiki a Lokacin amma kuma duk da haka wai sai sun yi yajin aikin.
Bukatun likitocin
Bukatun da likitocin ke neman wajen gwamnatin tarayya sun hada da biyansu alawus yayin da suke samun horo, inganta albashinsu sannan da biyansu albashinsu na watanni da gwamnati ba ta biya ba daga shekaran 2015.
Kungiyar na adawa da dokar da gwamnati za ta saka na ganin cewa sai likitoci sun yi aiki na tsawon shekara biyar kafin su iya ficewa daga kasar nan.
Discussion about this post