Cikin makon jiya ne aka fara sauraren shari’un ƙararrakin da wasu ‘yan takarar zaɓen shugaban ƙasa da jam’iyyun su, su ka maka APC, Bola Tinubu wanda ya yi nasara da kuma INEC a Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa, a Abuja.
Alƙalai biyar ne za su yi shari’ar, waɗanda aka ɗauko daga Kotunan Ɗaukaka Ƙara daban-daban a ƙasar nan.
Alƙalan Da Makomar Zaɓen Tinubu Ke Hannun Su:
Mai Shari’a Haruna Tsammani:
An ɗauko shi daga Abuja, kuma shi ne Shugaban Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Abuja. Shekarun sa 63.
Mai Shari’a Stephen Adah:
An ɗauko shi daga Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Asaba, babban birnin Jihar Delta. Shekarun sa 65.
Mai Shari’a Misitura Bolaji-Yusuf:
Shi ma daga Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Asaba da ke Jihar Delta aka ɗauko shine. Shekarun sa 63.
Mai Shari’a Moses Ugo:
An ɗauko Moses Ugo daga Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Kano. Ya na da shekaru 57.
Mai Shari’a Abba Mohammed:
An ɗauko Abba daga Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Ibadan, babban birnin Jihar Oyo. Shekarun sa 62.
Abubuwa 14 Dangane Da Alƙalan Shari’ar Zaɓen Tinubu:
1. Daga cikin su mace ɗaya ce, sauran huɗun maza ne.
2. Biyu daga cikin su su ne Shugabannin Kotun Ɗaukaka Ƙara a jihohin su.
3. Uku daga cikin su a Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria su ka yi digiri na farko. Ɗaya a Jami’ar Obafemi Awolowo, ɗaya kuma ta Ile Ife. Ɗaya kuma a Jami’ar Calabar.
4. An haifi huɗu daga cikin su kafin Najeriya ta samu ‘yanci. Ɗaya kuma bayan samun ‘yanci.
5. Dukkan su biyar ɗin sun halarci Makarantar Horon Aikin Shari’a ta Legas.
6. Wasu daga cikin su su na da hannu a wasu manyan shari’un da su ka haɗa da cire gwamna ba ta haramtacciyar hanya, wato tsohon Gwamnan Oyo, Rashidi Ladoja, cire Walter Onnoghen tsohon Babban Jojin Kotun Ƙoli, batun Nnamdi Kanu da shariar Gwamnan Kano mai barin gado, Abdullahi Ganduje. Sai shari’ar sauya wa Jami’ar Legas suna, ‘yancin mata ‘yan sanda, haramta Okada a Legas da wasu shari’u da dama.
7. Wannan ne karo na farkon dukkan su da za su yanke hukunci a shari’ar zaɓen shugaban ƙasa.
8. Wasun su sun shafe shekaru 39 su na aikin shari’a. Wasu kuma sun kai har shekaru 41.
9. Wasu shekarun 13 su na alƙalanci a Babbar Kotu. Wasu kuma sun shafe shekaru har 24.
10. A cikin su akwai Mai Shari’a matsayin na 12 wasu kuma akwai wanda ya kai har matsayi na 71 a jerin darajojin manyan Alƙalan Kotun Ɗaukaka Ƙara.
11. Sun yi aiki a matsayin Alƙalan Kotun Ɗaukaka Ƙara daga shekaru biyu da su ka gabata zuwa tsawon shekaru 12.
12. An zaɓo su ne daga yankuna biyar cikin shida na yankunan shiyyoyin Najeriya.
13. Wasu daga cikin su sun yi ƙaurin suna a kakafen yaɗa labarai, wasun su kuwa ba a san su ba, ba a jin ɗuriyar su.
14. An ba su nan zuwa watan Satumba su yanke hukunci. Daga nan duk ɗan takarar da bai amince ba, sai ya garzaya Kotun Ƙoli.
Discussion about this post