Kakakkin ƴan sanda Najeriya Muyiwa Adejobi ya bayyana cewa wasu dalilai da ya sa Hedikwatar ƴan sanda na kasa ta kama ƴan sandan da ke rufa wa mawakin Buhari da APC baya, wato masu tsaro cewa ƴan sandan sun yi ganganci ne a wurin aikin su.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa ta facebook, Adejobi ya ce ƴan sandan ba su nuna dattaku da kwarewa a aikin su ba a lokacin da suka rika ɓarin wuta domin tarwatsa jama’a da nuna isa da izza da suka yi don suna gaɗin mawaƙi Rarara.
Adejobi ya ce “An gano duka ƴan sandan kuma an kama su. Za a yi musu tambayoyi sannan lallai za a ɗauki mataki akan su domin sun nuna rashin kwarewa a aikin su ƙarara.
A wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta, a yanar gizo, an ga ƴan sandan suna harbi sama a lokacin da Rarara zai shiga motar sa a garin Kahutu.
Sai dai kuma shi Rarara ya ce ba don nishaɗi ko nuna isa ne ko kuma wai don a kwarzanta shi ne ƴan sandan suka yi harbi sama ba a lokacin da zai shiga mota.
Rarara ya ce ” Ko da muka gama raba kayan tallafi a garin Kahutu na azumi, an samu hasashen cewa wasu matasa na so su tada tarzoma a wurin, dalilin haka ne ya sa ƴan sandan suka tsorata su da harbi a sama.
Rarara ya kara da cewa abinda ya sa basu harba barkonun tsohuwa ba shine don mutane na azumi.
Sai dai kuma wannan hujja da Rarara ya bada akwai yiwuwar ba zai yi tasiri ba domin maganan tsaro abinda ya dace ake yi wato abinda shari’a ya gindaya ba abinda ake so ba.
Wani maikaratu, mai suna Gambo Lawan, da yake tofa albarkacin bakin sa, ya ce, ” Tabbas waɗannan ƴan sanda sun tafka ganganci, ai ba son rai ake yi ba a aikin tsaro, abinda ya dace doka ta ce ake yi. Idan har abinda suka yi sai an harba barkonun tsohuwa ne to ai haka za a yi, ba barnata harsashin da gwamnati ke siya da kuɗin ƴan kasa ba.
Sannan kuma idan ka kalli bidiyon za ka ga su kan su ƴan sanda sun yi haka ne don su kwarzanta mawakan domin hatta matanen da suka biyo shi kirari suke ma sa
Discussion about this post