Idan ba a manta ba tun bayan furta cewa magoya bayan Peter Obi da ake kira Obidients, masu ra’ayin rikaune ne da Wole Soyinka yayi a hira da ya yi da talabijin din Channels mutane da dama ke ta maida masa da martani, musamman ƴan bangaren jam’iyyun adawa na PDP da LP.
Tun bayan sanar da sakamakon zaben shugaban kasa da aka yi a watan Faburairu magoya bayan musamman Peter Obi da ake kira Obidients ke fitowa suna fadin an yi wa ɗan takarar su murɗiya ne a zaɓen.
A wata faifan murya da aka bankado an ji Obi na rokon fitataccen Fasto Oyedepo ya yi kira ga Kiristoci su zaɓe shi domin tafiyar tasa jihadi ce tsakanin Kiristanci da Musulunci.
Soyinka ya ce da kan sa ya fadi wa Obi cewa idan ya fadi zaɓe, to kada yayi kuka da kowa ya yi kuka da magoya bayan sa ne. Sune suka sa ya fadi zabe.
Bayan waɗannan kalamai na sa, fitacciyar marubuciya Chimamanda ita ma ta fito da nata salon martanin inda ta rubuta buɗaɗɗiyar wasika ga shugaban Amurka Joe Biden cewa kada ya ta ya Bola Tinubu murnar lashe zaɓen shugaban kasa.
A cewar ta an yi wa Peter Obi murɗiya ne a zaɓen, shi ya sa bai yi nasara ba.
Bayan hirar Soyinka, Charlie Boy shima ya soke Farfesan inda ya ce daga yanzu sun yi hannun riga dashi babu sauran mutunci tsakaninsa da shi saboda kalaman da yayi kan ƴan Obidients.
Shima tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani ya tofa albarkacin bakin sa akan badaƙalar.
A rubutu da ya saka a shafin sa ta tiwita, Shehu Sani ya yi ikirarin cewa ” Idan ba a kira waɗanda suka babbake gidajen ƴan adawa da kashe ƴan PDP saboda Buhari ya fadi zaben 2011 ba, ba za a kira magoya bayan Peter Obi masu ra’ayin riƙau ba.
Shehu Sani ya ce ” A 2011 duk wani dan Arewa mai adawa da Buhari an ɗauke shi a matsayin kafiri ne. Bayan zaben, ƴan takife sun tayar da tarzoma, suka rika bin gidajen ƴan jam’iyyar PDP, suna babbakewa sannan suna kashe ‘yan uwansu, idan ba a kira su masu ra’yin rikau dake neman tada zaune tsaye ba, ba ko za a yi wa ƴan Peter Obi laƙani da haka ba.”
Discussion about this post