Zaɓaɓɓen shugaban kasa, Bola Tinubu ya bayyana wa dandazon masoyan sa da suka ɗunguma filin jirgin saman Abuja domin tarban sa cewa ya dawo da karfin sa kuma cikin koshin lafiya domin soma aikin gyara Najeriya gadan-gadan.
Idan ba a manta ba Tinubu ya fita zuwa kasar Birtaniya inda da daga can ya garzaya kasar Saudiyya domin yin da aikin Umrah.
Da yake jawabi ga dubban jama’a da suka dunguma zuwa wajen tarban sa, Tinubu ya ce ” Na huta sosai kuma yanzu da ƙarfi na da dawo Najeriya kuma cikin koshin lafiya.
” A lokacin da nake hutu, na gana da mutrane da dama da masu ruwa da tsaki domin shirya tunkarar mulkin Najeriya gadan-gadan ba tare da an samu jinkiri ko da ko na sakan ɗaya ne ba.
Mataimakin sa Kashim Shettima, tsohon shugaban hukumar EFCC, Nuhu Ribadu da wasu daga cikin jigajigan APC na daga cikin waɗanda suka tarbeshi a filin saman Abuja.
Discussion about this post