Wata kungiya ta magoya bayan APC a Kano ta ce NNPPin Kano ba ta so a bai wa Yankin Arewa maso Yamma muƙamin Shugaban Majalisar Dattawa, saboda Sanata Barau Jibrin da ke neman muƙamin.
Kakakin NNPP, Abdulmumin Jibrin, kuma zaɓaɓɓen ɗan majalisar tarayya daga Kano, ya bayyana cewa bai kamata a bai wa Musulmi kuma ɗan Arewa shugabancin Majalisar Dattawa ba, saboda adalci bai ce haka ba.
A ranar Laraba ce Jibrin ya ce dokar 1999 ta nuna cewa kamata ya yi shugaban majalisar dattawa ya fito daga Kudu maso Gabas.
Sai dai kuma a cikin wani raddin gaggawa da wata ƙungiyar ‘Rescue North-west APC ta fitar tare da sa hannun Shugaban Ƙungiya, Muktar Gora, ya ce Abdulmumin Jibrin ya yi magana ce kawai saboda ya na jin tsoron kada Sanata Barau Jibrin ya zama shugaban majalisar dattawa.
Gora ya ce NNPP a Kano ta san idan Sanata Jibrin ya zama shugaban majalisar dattawa, to APC za ta ƙara ƙarfi a Arewa maso Yamma, sauran ƙananan jam’iyyu kuma irin su NNPP za a neme su a rasa.
Ya ce shi bai ga dalilin da zai sa NNPP a Kano ta kawo batun addini a zaɓen shugaban majalisar dattawa.
Daga nan Gora ya shawarci Abdulmumin Jibrin ya koyi darasin iya siyasar ci gaba.
Discussion about this post