Ɗan takarar shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya zargi Hukumar Zaɓe cewa ta hanyar maguɗi ta rika kakkaftar kuri’un sa tana lallafta wa Tinubu da gangar don ya ci zaɓe.
Atiku ya ce zai gayyaci duka kamfanonin da ke da hannu wajen kirkiro da na’urar BVAS da samar masa da Internet wata kamfanin Kaspersky da Globacom, su bayyana a kotu domin bada shaida.
Bayan haka, Zai gayyaci ICRC, shima ya zo ya bada shaida a lokacin da za a fara zaman sauraren karar.
Atiku ya kara da cewa abinda shugaban Hukumar Zaɓe yayi na bayyana sakamakon zaɓen da aka yi ba gaskiya bane, ” Kawai ya kakkafto kuri’u na ne ya rika laftawa Tinubu kawai har ya ci zaɓe. Saboda haka ni ban yarda.
A karshe dai Atiku ya ce ko dai Kotu ta ayyana shi shugaban kasa ko kuma kawai a sake zaɓe, hakan shine zaman lafiyar kowa da kowa.
Hakan shima Peter Obi na LP ya ce shine ya ci zaɓen ba Tinubu ba.
Tuni shi kansa Obin ya garzaya Kotu domin kalubalantar zaɓen.
Ya ce ba maganar sake zaɓe ya ke yi ba, shine ya ci zaɓe tangararas, kawai a kwace nasara daga Tinubu a bashi.
Discussion about this post