Wasu mazauna jihar Kaduna a ranar Laraba sun yi kira ga Sabon gwamnan jihar Uba Sani da ya fi maida hankali wajen samar wa talakawa ruwan sha a fadin jihar.
Mazaunan da suka yi wannan kira a hiran da suka yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ranar Laraba su ce rashin ruwa ya zama babban matsalar da abin tashin hankali a jihar.
Wani mazaunin garin Kaduna Martins Dangwa ya ce mutane da dama sun dade rabon da su ga ruwan fanfo yana mai cewa duk hanyoyin da gwamnati ta bijiro dasu domin a samu wadatar ruwan fanfo ya citura domin bai haifar wa mutanen Kaduna da mai ido ba.
Wata mai suna Gloria Bulus ta yi kira ga mutane da duk a taru a cigaba da tunatar da gwamnati game da wannan matsala na rashin ruwan Fanfo ada ake fama dashi a jihar.
“Yanzu da muka zabi sabbin shugabanni muna rokon su da su maida hankali wajen tabbatar da ababen more rayuwa sun wanzu a fadin jihar.
Daga nan kodinatan kungiyar Ruwa da tsaftace muhalli na jihar Kaduna Rev Kuzasuwst Peter ya yi kira ga gwamnati da ta kara inganta samar da ruwa a jihar.
Peter ya ce inganta Samar da ruwan sha da tsaftace muhalli musamman a cikin kauyuka na daga cikin hanyoyin inganta aiyukkan sauran fannoni a jihar.
Discussion about this post